TARIHIN NURA M. INUWA

Takai Taccen Tarihin Mawaki Nura M
Inuwa Tattaunawa Kai Tsaye Tafeda
Jarumi Abas Sadiq Cikin Shirin Gani
Da Idonka.
ABBAS SADIQ : Da farko dai masu
Sauraro zasuso suji takai taccen
tarihinka?
Nura M Inuwa : Da farko dai sunana
Nura Musa Inuwa wanda a yanzu
akafi sani da Nura M Inuwa, Ni
Haifaffen Garin Kano ne Gommaja
Karamar Hukumar Dala.
Nayi Makaranta na na primary school
a masaka special primary school
daganan na wuce Gommaja two inda
inda acan nayi secondry school dina
daga nan kuma cikin ikon ubangiji
banci gaba ba, Daganan sai na fara
harkar waka.
ABBAS SADIQ : Nura M Inuwa me
yaja hankalin kane har ka fara harkar
waka.
Nura M Inuwa : Aah! Alhamdulillahi
Nidai tun farko bani da wani dalili da
yaja hankalina na fara harkar waka,
sabo da ya samo asaline tun ina yaro
ni kaina haka kawai inayin waka haka
kuma idan akan batamun raj nakanyi
waka domin in huce bacin ran nan da
akamun hakama idan an faranta mun
nakanyi waka.
Ta yadda tun bansan kalar ko launin
wakaba da yadda take nidai kawai
inayi, daga baya kuma saina sawa
raina cewa inason in fara waka, ina
girma ina girma sai nazo na fara
Makaranta, Sabo da haka Allah cikin
ikon sa sai na fara waka a Makaranta
inda nakanyi waka ta Yabo
musamman in ana Maulidi inzo in
rera a haka a haka abu yanaci gaba.
Kancewar ba wakar Yabon na fara
yiba, Sai akazo idan na kalli Film
"Misali" Ace wannan Film din na daya
ne lokacin ana yin film pert 1 and 2
to a lokacin sai ya zamana ina iya
kirkirar waka ta kaina idan na kalli
film na daya kuma ya burgeni to sai
in kirkiri waka tawa ta kaina wacce
nake ganin itace zata zama ci gaban
wannan shirin film din.
Da haka da haka inayi Allah cikin
ikonsa har nazo na fara Waka dana
farane kuma sai na fahimci cewa zan
iya daukar waka a mastayin haryace
ta tura sakon ni na fadakarwa sannan
kuma zan iya rikanta a matsayin
sana'a kamar yadda take yanzu a
wurina.
Wannan Shine Kadan Daga Cikin
Abunda Muka Dan Tsakuro Muku
Dangane Da Tarihin Mawaki Nura M
Inuwa, Akwai Yiwuwar Ci Gaba Da
Kawo Muku Wannan Tattaunawa Nan
Bada Jimawa Ba.

I BUILT MY SITE FOR FREE USING