Umar Muhammad Sharif fitaccen
mawakin fina-finan Hausa ne, a hirar
da ya yi da Aminiya a ranar Lahadin
da ta gabata ya bayyana yadda ya
fara waka da irin nasarorin da ya
samu da kuma wasu daga cikin
kalubalen da ya fuskanta:
Tarihina a takaice
Assalamu alaikum, sunana Umar
Muhammad Sharif,
an haife ni a Rigasa da ke Jihar
Kaduna a shekarar 1987. Na yi
makarantar firamare da sakandare
duk a Rigasa.
Dalilin da ya sa na zabi sana’ar waka
Waka ta fado mini kwatsam da rana
tsaka ne, amma a gaskiya ban taba
tunanin zan yi sana’ar waka ba,
saboda tun tasowata ni dalibi ne, ina
karatun boko da na addini, na ma fi
ba da karfi a bangaren addini. Silar
fara waka kuwa ita ce akwai wata
budurwa da nake matukar so da
kauna, amma na kasa sanar da ita
abin da ke zuciyata. A gaskiya jin
nauyin abin shi ne ya hana ni sanar
da ita. Nakan je har kofar gidansu, na
aika a yi mini sallama da ita, amma
inda gizo ke sakar shi ne da zarar ta
fito don ganin wanda ke neman ta,
sai na buya, ta gama dube-dubenta
daga nan idan ba ta ga kowa ba sai
ta koma gida. To na yi hakan kusan
har sau uku ba tare da samun damar
tsayawa da ita ba. Daga nan wata
rana sai na yi ta maza na ce zan ga
abin da zai ture wa buzu nadi. Da na
je sai na aika kamar yadda na saba
amma sai a wannan karon ba ta fito
ba. Na yi ta jira amma shiru kake ji.
To daga nan ne fa kamar wasa sai na
fara yin waka a kan halin da na samu
kaina ciki. Daga kofar gidansu na fara
waka har na isa gida ban daina ba.
Haka na yi tayi duk lokacin na tuna
da wannan baiwar Allah.
A cikin wannan halin ne sai na samu
biro da takarda na rubuta wakar.
Akwai wani mawaki Ibrahim Suleiman
(Zaki) wanda ya kasance abokin
yayana ne. Kamar wasa da ya ga
wakar kuma ya umarce na rera ta.
Bayan ya saurari wakar sai ya yaba
kuma ya yi min wasu gyararraki, kana
ya karantar da ni kabli da ba’adin
waka. Daga nan ne fa na fara waka
gadan-gadan.
kalubale
Da farko na fuskanci kalubale daga
gida, daga bisani muka fahimtar da
iyayenmu. Bayan ba su ga canji daga
irin tarbiyyar da suka yi mana ba, sai
suka fara sa mana albarka da fatan
alheri. Shakka babu addu’o’insu na
tasirin sosai a kan nasarorin da muke
ci gaba da samu.
Wakokin da na yi
A kalla wakokina za su kai 500
Kundin waka
Akwai su kamar haka: ‘Duniya Ce’ da
‘Nadiya’ da ‘Shahuda’ da ‘Madubi da
‘Mai Atamfa’ da kuma ‘Babbar
Yarinya’
Bakandamiyata
Duka wakokina.
Fitowa a fim
Ina fitowa a fim, sannan nakan shirya
nawa. Fina-finan da na fito sun hada
da: ‘Mahaifiyata’ da ‘Nas’. Fina-finan
da na shirya sun hada da: ‘Ba Zan
Barki Ba’ ’Ka So A So ka’ da ’Jinin
Jikina ’
Burina
Ba ni da wani burina saboda ko
yanzu kasuwa ta watse dan koli ya ci
riba. Sunana ya kai duk inda ba ka
zato, saboda na sha samun kira ta
waya daga Amurka da sauran
kasashen duniya, wanda jama’a ne
masu sauraren wakokinmu ke yaba
mana.
Iyali
Ina da mata daya Maryam da da daya
ana kiransa Aliyu.